Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Yayin da yake jawabi ga daliban, Jagora (H) ya bayyana Shahadar Sayyid Khamenei (RH) wadda ta auku a watan Shahadar Amirulmumin (AS), wato watan Ramadan, kuma aka bizne shi a daren Shahadar Imam Zainul Abidin (AS) a matsayin wani abu na hikimar Allah Ta'ala, wanda bai zama bisa hadari ba. Yace, wannan kuma ya nuna hanyar dai kenan, hanyar Shahada wadda ta kiɗima maƙiya, suka kasa ganewa.
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana yadda kullum makiya ke ganin kamar in suka kashe A'alam daga cikin mutane, kamar sun kashe addini ne. Inda ya nanata maganar da ya wa wasu jami'an tsaro bayan Wakiar Buhari. Yace, “Ku a tsammaninku in kun kashe mutum za ku kawar da abu ne. To da kashe wani mutum zai kawar da Shi'a, to da wannan mutumin Imam Husaini (AS) ne. To amma kashe shi sai ya tambatsa Shi'a.”
Jagora ya bayyana cewa, har yanzu al'amarin haka yake, duk abinda maƙiya suka yi, sai dai su tambatsa. Yace: "Ballantana ni ƙaramin alhaki, wanda in kun kashe ni, sai dai ku ƙara yawan Shahidan Karbala.”
Ya bayyana yadda tunanin makiya ya nuna musu cewa, in sun kashe Sayyid Khamenei shi kenan. “Maimakon haka, sai suka ga sun raya shi ne.”
Da ya juya bangaren nasiha ga daliban, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana musu cewa, dukkansu, maza da mata da yaransu sun zo diban ruwa ne, za su je su shayar da gida. “Don a gida ana matukar kishin ruwa (na ilimin tafarkin Ahlulbait (AS).
Ya bayyana yadda tsawon zamani aka haramta ma yankinmu sanin tafarkin Ahlulbaiti (AS), yace, amma yanzu cikin garejen lokaci abin yana haɓɓaka.
Jagora (H) ya kawo misalai na irin dakewar Amirulmumin (AS) a tarihi, da kuma yadda mabiyansa a jiya da yau suka kasance jarumai wajen bayar da kariya ga addinin Musulunci. Yace: “(Wannan shi ne Tafarkin waɗanda suke dakewa, waɗanda su a wurin su a kashe ka a tafarkin Allah ɗaukaka ce.
“Darajan wanda aka kashe a cikinmu, yana zama ne daram a zukatanmu, tasirinsa ma sai ya fi (yawa) bayan Shahadarsa, fiye da lokacin da yake da rai, kamar yadda muka gani a Shahadar Sayyid Qa'id, wanda da yawan mutane sai bayan Shahadar shi suka gane waye wannan bawan Allah din.”
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada cewa: “Wannan makaranta ta sadaukarwa (ita ce kawai mafita). Duk wani wanda zai ce maka akwai wata dabara, ko wata hanya ta daban, ko wani yanke, wanda akan bi cikin sauƙi a cimma nasara, to kace da shi, in dai dabara ce, da Imam Husaini (AS) ya yi wannan dabaran, da sauran mabiyansa ma sun yi dabaran. Har ma yanzu abinda muke gani, da abin dabara ne, shi ma sai mu ce, da Sayyid Qa'id shi ma sai ya yi dabara. Amma al'amarin sadaukarwa ne. Tsayawa ne ƙyam a tafarkin Allah, sai dai Allah ya yi hukuncin.”
Sayyid Zakzaky ya jaddada cewa: “Kuma mun san cewa muna da wani garanti, mun san cewa ba yadda za a yi a murkushe mu. Mu fa ba masu murƙusuwa ba ne. Ba kawai ba za mu murƙusu ba ne, mu ne ma masu murƙusarwa. Nasara tamu ce, ko mutum ya ƙi, ko ya so, don muna tare da Wanda ke ba da nasara. Insha Allah.”
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
29/Muharram/1448
14/07/2026
Ra'ayinka